Mon

26

May

2014

Sayyid Nasrallah: Gwagwarmayar Musulunci Ta Hana Kafuwar Sabuwar Gabas ta Tsakiya

12- Hausa

Babban sakataren Kungiyar Hizbullah  ya ce; A duk lokacin da H.k. Isra’ila ta wuce gona da iri akan kasar Lebanon da al’umma za su fuskanci maida martani daga gwagwarmaya. Sayyid Hassan Nasrullah wanda ya yi jawabi dazu a wurin bikin zagoyowar cin nasarar gwagwarmaya akan yahudawan sahayoniya, ya bayyana cewa; Nasarar da aka samu ta korar ‘yan sahaniya ta zama ginshikin samun wasu nasarori masu yawa da su ka biyo baya,kuma ta kawo karshen shirin Amurka da h.k. Isra’ila na kafa sabuwar gabas ta tsakiya. Sayyid Hassan Nasarallah ya ci gaba da cewa; Nasarar da gwagwarmaya ta samu akan  nasara ce ga dukkanin al’ummar Lebanon da larabawa da musulmi, domin babu wata kungiya da za ta riya cewa nasararta ce ita kadai. Babban magatakardar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ya kuma ce; matukar babu wani kyakkyawan tanadi na tsaron kasar Lebanon  daga gwamnati gwagwarmayar Musulunci za ta ci gaba da kare kasa.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/24614-sayyid-nasarallah-gwagwarmayar-musulunci-ta-hana-kafuwar-sabowar-gabas-ta-tsakiya-ta-amurka

Read More 0 Comments

Sun

30

Mar

2014

Sayyid Nasrallah: Karfin Kungiyar Hizbullah Ya Rubanya Irin Na Baya

22- Hausa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a halin yanzu ya rubanya wanda take da shi a baya yana mai cewa kungiyar za ta ci gaba da tsayawa kyam wajen kare kasar daga wuce gona da irin HKI.    

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya yi a daren jiya a wajen bikin bude wata cibiya ta al’adu da kungiyar ta gina inda ya ce dakarun Hizbullah din sun sami nasarar ‘yanto wasu yankuna na kasar Labanon albarkacin irin tsayin dakansu.

Yayin da ya koma kan batun shiga kasar Siriya da dakarun Hizbullah suka yi don fada da kungiyoyi masu kafirta musulmi da aka turo kasar, Sayyid Nasrallah ya sake jan kunne dangane da hatsarin da ke tattare da irin wadannan kungiya wanda ya ce idan suka yi nasara a Siriya to kuwa za su kawar da kowa ne wanda bai yi tarayyar da su cikin ra’ayi ba.

Sayyid Nasrallah ya yi watsi da batun da wasu suke kawowa na yiyuwa HKI ta kawo wa Labanon hari inda ya ce a halin yanzu dai HKI ba ta da jaruntakar aikata hakan don kuwa ta san me ke jiranta.

http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/23887-sayyid-nasrallah-karfin-kungiyar-hizbullah-ya-rubanya-irin-na-baya

Read More 0 Comments

Sat

21

Dec

2013

Hizabullah ta sha alwashin daukar fansa akan wadanda su ka kashe kwamandanta

13Hausa

Shugaban Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ke kasar Lebanon, Sayyid Hassan Nasarallah ya ce; Za su dauki fansa akan h.k. Isra’ila dangane da kisan daya daga cikin kwamandojin gwagwarmaya. Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi dazu a birnin Beirut dangane da juyayin shahadar Alhaj Hassan al-LAqis, ya ce; Ko ba dade ko bajima za a dauki fansa akan makasansa.” Jagoran kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa; H.K. Isra’ila tana kuskure idan har tana tsammanin cewa Hizbullah yana cikin matsala, kuma abinda na ke fadawa Isra’ila shi ne cewa; Wadanda su ka kashe Shahid Laqis ba za su kasance a cikin aminci ba a ko’ina su ke a duniya, domin lokacin daukar fansa yana tafe.” Da ya koma magana akan hare-haren bayan nan da ‘yan alkaeda su ka kai wa sojojin kasar ya yi kira da bada cikakken goyon baya ga sjojin domin su ke garkuwar kasar.

 

http://hausa.irib.ir/labarai/item/22785-lebanon-hizabullah-ta-sha-alwashin-daukar-fansa-akan-wadanda-su-ka-kashe-kwamandanta

Read More 0 Comments

Tue

29

Oct

2013

Saudiyya Tana Cikin Fushi Saboda Cimma Manufarta A Siriya

13Hausa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kasar Saudiyya tana cikin tsananin fushi sakamakon rashin cimma manufarta ta kifar da gwamnatin Siriya duk kuwa da kokarin da ta yi ba dare da ba rana wajen cimma wannan manufar.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin tunawa da shekaru 25 da kafa asibitin Rasulul A’azam a kasar Labanon inda yayi ishara da shan kashin da kasashen da suke adawa da gwamnatin kasar Siriya suke fuskanta a kokarin da suke yi na kifar da gwamnatin kasar wanda ya ce hakan shi ne ya fusata kasar Saudiyya sakamakon gazawar da ta yi na cimma manufarta ta kifar da gwamnati ta hanyar amfani da dukiya da kuma ‘yan ta’addan da take shigo da su Siriya daga kasashe daban-daban na duniya

http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/22249-sayyid-nasrallah-saudiyya-tana-cikin-fushi-saboda-cimma-manufarta-a-siriya

Read More 0 Comments

Tue

24

Sep

2013

Ya kira yi kasashen Saudiyya da Turkiya da su sauya siyasarsu

15- Hausa

Shugaban Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa; suna da kwararan dalilai akan wandanda su ka kai hari a unguwar Dhahiya da ke kudancin birnin Beirut.

A jawabin da ya gabatar dazunnan, Sayyid Hassan Nasrallah ya ce; wadanda su ka kai harin masu akidar kafirta musulmi ne, kuma suna da alaka da ‘yan tawayen kasar Syria. Jagoran na kungiyar Hizbullah ya kuma  yi ishara da tsokacin da shugaban kasar Turkiya Abdullah Gul ya yi, akan hatsarin da ke tattare da masu akidar kafirta musulmi a kasar Syria, sannan ya kara da cewa; An sanar da Gul ne cewa abinda ya ke faruwa a cikin kasar Pakistan zai iya faruwa a cikin Turkiya. Da ya ke maida martani akan zargin da ‘yan hamayyar Syria su ka yi na cewa; gwamnatin Syria ta bai wa Hizbullah makamai masu guba, Sayyid Nasarallah ya ce; Akida ta addini da kungiyar Hizbullah ta ke riko da ita, ta haramta mata mallaka balle amfani da wadannan irin makaman.

Har ila yau, Sayyid Nasrallah, ya yi ishara da cin kasar da kasashen da ke goyon bayan ‘yan ta’adda a Syria su ka yi, na kasa kifar da gwamnati, abinda ya ingiza su ga yin tuhuma mara tsuhe da cewa; HIzbullah ta mamaye Syria. Jagoran na Hizbullah ya ce babu wanda zai gaskata cewa kungiyar ta Hizbullah tana da karfin da za ta iya  mamaye  kasa kamar Syria. Jagoran kungiyar ta Hizbullah ya yi kira ga kasashen Saudiyya da Turkiya da su sake siyasarsu ta ina- da- yaki, domin kuwa yanayin siyasar yanki da duniya baki daya ya sauya.   

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21888-sayyid-hassan-nasrallah-ya-kira-yi-kasashen-saudiyya-da-turkiya-da-su-sauya-siyasarsu

0 Comments

Sat

17

Aug

2013

Sayyid Hasan Nasrullahi Ya Bayyana Hatsarin Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kudancin Labanon

13- Hausa

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya bayyana harin da aka kai kudancin kasar Labanon da cewar harin ta'addanci ne mai hatsari.     

A jawabin da ya gabatar a bikin tunawa da gagarumar nasarar da kungiyar Hizbullahi ta samu a yakin kwanaki 33 da ta yi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin watan Yulin shekara ta 2006 a garin Aita-Sha'ab da ke kudancin kasar Labanon a yau Juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar ga dukkan alamu masu dauke da ra'ayin kafirta musulmi ne suka aiwatar da harin ta'addancin da aka kai kudancin birnin Beiruit a jiya Alhamis da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 22 tare da jikkata wasu 330 na daban.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21483-sayyid-hasan-nasrullahi-ya-bayyana-hatsarin-harin-ta-addancin-da-aka-kai-kudancin-labanon

Read More 0 Comments

Sat

03

Aug

2013

Sayyid Nasrullahi Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Haramtacciyar Kasar Isra'ila

14- Hausa

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon ya jaddada cewar haramtacciyar kasar Isra'ila barazana ce ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, don haka shafe ta daga kan doron kasa masalaha ce ga dukkanin kasashen yankin.

A jawabinsa ga dubban jama'a a yayin taron gangamin ranar Qudus ta duniya a kudancin birnin Beirut na kasar Labanon a jiya Juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi ya jaddada cewa; dole ne al'ummar musulmin duniya su fi ba da fifiko kan batun 'yantar da Palasdinu saboda haramtacciyar kasar Isra'ila ba kawai barazana ce ga Palasdinu ba, domin cutar kansa ce mai yaduwa da take da mummunar hatsari ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21331-sayyid-nasrullahi-ya-jaddada-wajabcin-kawo-karshen-haramtacciyar-kasar-isra-ila

Read More 0 Comments

Thu

25

Jul

2013

Ya Yi Watsi Da Matakin Kungiyar Tarayyar Turai A Kan Hizbullah

18- Hausa

Babban magatakardar Kungiyar HIzbullah Sayyid Hassan Nasarllah ya yi watsi da matakin tarayyar turai wanda ya shigar da kungiyar ta gwagwarmaya a karkashin sunayen 'yan ta'adda. A wani jawabi da jagoran na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ya yi a yayin bud-bakin shekara-shekara, Sayyid Hassan Nasarallah ya ci gaba da cewa; Abu guda mai muhimmanci  shi ne cewa kungiyar tana da cikakken goyon bayan al'ummarta.

Jawabin na Sayyid Hassanrallah shi ne na farko bayan da kungiyar tarayyar turai ta shigar da bangaren soja na kungiyar Hizbullah a karkashin sunayen kungiyoyin ta'adda. Ya kuma bayyana cewa babu wata moriya da turai za su ci daga wannan matakin da suka dauka. Dangane da cikin gida Lebanon kuwa, Sayyid Nasarallah ya kirayi masu adawa da Hizbullah da su kwana da sanin cewa ba za su iya amfani da wannan matakin ba domin cin moriyarsa a siyasance.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21233-sayyid-hassan-nasrullah-ya-yi-watsi-da-matakin-kungiyar-tarayyar-turai-a-kan-hizbullah

Read More 0 Comments

Mon

17

Jun

2013

Abin Dake Gudana A Siriya Ba Yaki Ne Tsakanin Shi'a Da Sunna Ba

15- Hausa

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tunawa da ranar dakarun kungiyar da suka sami rauni a wajen gwagwarmaya inda yace masu kokarin yada irin wadannan maganganu na cewa abin da ke faruwa a kasar Siriya musamman bayan shigowar dakarun kungiyar Hizbullah kasar wani rikici ne na Sunna da Shi’a wani kokari ne da suke yi na nuna fushinsu dangane da irin kashin da suka sha a yakin garin Qusayr da dakarun siyasa suka kwato daga hannun ‘yan ta’adda.

http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/20849-sayyid-nasrallah-abin-dake-gudana-a-siriya-ba-yaki-ne-tsakanin-shi-a-da-sunna-ba

Read More 0 Comments

Sun

26

May

2013

Nasrullahi Ya Bayyana Hatsarin Amurka Da 'Yan Ta'addan Siriya A Kan Al'ummar Musulmi Da Kirista

20- Hausa

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya jaddada cewar kasar Siriya ita ce kashin bayan gwagwarmaya don haka 'yan gwagwarmaya ba zasu taba zuba ido suna ganin ana neman karya kashin bayansu ba.    

http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/20577-nasrullahi-ya-bayyana-hatsarin-amurka-da-yan-ta-addan-siriya-a-kan-al-ummar-musulmi-da-kirista

Read More 0 Comments

Thu

02

May

2013

Sayyid Nasrallah: Kawayen Siriya Ba Za Su Taba Bari Ta Fadi Ba

21- Hausa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewar ya kamata kasashen yammaci su fahimci cewa kasar Siriya tana da kawaye na hakika wadanda ba za ta taba bari a kifar da gwamnatinta kasar ba.
Read More 0 Comments

Sun

17

Feb

2013

Sayyid Nasrullah Ya Ce Fahimta Da Yin Aiki Da Koyarwar Manzon Allah (SAW) Ita Ce Mafita

Hausa

Sayyid Nasrullah Ya Ce Fahimta Da Yin Aiki Da Koyarwar Manzon Allah (SAW) Ita Ce Mafita

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, babu banbancin manufa a tsakanin dukkanin bangarorin siyasar haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummomin larabawa da musulmi.  

http://hausa.irib.ir/labarai/item/19319-sayyid-nasrullah-ya-ce-fahimta-da-yin-aiki-da-kiyarwar-manzon-allah-saw-ita-ce-mafita

 

 

 

 

 

 

 

0 Comments