Sayyid Nasrallah: Gwagwarmayar Musulunci Ta Hana Kafuwar Sabuwar Gabas ta Tsakiya

12- Hausa

Babban sakataren Kungiyar Hizbullah  ya ce; A duk lokacin da H.k. Isra’ila ta wuce gona da iri akan kasar Lebanon da al’umma za su fuskanci maida martani daga gwagwarmaya. Sayyid Hassan Nasrullah wanda ya yi jawabi dazu a wurin bikin zagoyowar cin nasarar gwagwarmaya akan yahudawan sahayoniya, ya bayyana cewa; Nasarar da aka samu ta korar ‘yan sahaniya ta zama ginshikin samun wasu nasarori masu yawa da su ka biyo baya,kuma ta kawo karshen shirin Amurka da h.k. Isra’ila na kafa sabuwar gabas ta tsakiya. Sayyid Hassan Nasarallah ya ci gaba da cewa; Nasarar da gwagwarmaya ta samu akan  nasara ce ga dukkanin al’ummar Lebanon da larabawa da musulmi, domin babu wata kungiya da za ta riya cewa nasararta ce ita kadai. Babban magatakardar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ya kuma ce; matukar babu wani kyakkyawan tanadi na tsaron kasar Lebanon  daga gwamnati gwagwarmayar Musulunci za ta ci gaba da kare kasa.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/24614-sayyid-nasarallah-gwagwarmayar-musulunci-ta-hana-kafuwar-sabowar-gabas-ta-tsakiya-ta-amurka

Write a comment

Comments: 0