Sayyid Nasrallah: Karfin Kungiyar Hizbullah Ya Rubanya Irin Na Baya

22- Hausa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a halin yanzu ya rubanya wanda take da shi a baya yana mai cewa kungiyar za ta ci gaba da tsayawa kyam wajen kare kasar daga wuce gona da irin HKI.    

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya yi a daren jiya a wajen bikin bude wata cibiya ta al’adu da kungiyar ta gina inda ya ce dakarun Hizbullah din sun sami nasarar ‘yanto wasu yankuna na kasar Labanon albarkacin irin tsayin dakansu.

Yayin da ya koma kan batun shiga kasar Siriya da dakarun Hizbullah suka yi don fada da kungiyoyi masu kafirta musulmi da aka turo kasar, Sayyid Nasrallah ya sake jan kunne dangane da hatsarin da ke tattare da irin wadannan kungiya wanda ya ce idan suka yi nasara a Siriya to kuwa za su kawar da kowa ne wanda bai yi tarayyar da su cikin ra’ayi ba.

Sayyid Nasrallah ya yi watsi da batun da wasu suke kawowa na yiyuwa HKI ta kawo wa Labanon hari inda ya ce a halin yanzu dai HKI ba ta da jaruntakar aikata hakan don kuwa ta san me ke jiranta.

http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/23887-sayyid-nasrallah-karfin-kungiyar-hizbullah-ya-rubanya-irin-na-baya

Write a comment

Comments: 0