Hizabullah ta sha alwashin daukar fansa akan wadanda su ka kashe kwamandanta

13Hausa

Shugaban Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ke kasar Lebanon, Sayyid Hassan Nasarallah ya ce; Za su dauki fansa akan h.k. Isra’ila dangane da kisan daya daga cikin kwamandojin gwagwarmaya. Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi dazu a birnin Beirut dangane da juyayin shahadar Alhaj Hassan al-LAqis, ya ce; Ko ba dade ko bajima za a dauki fansa akan makasansa.” Jagoran kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa; H.K. Isra’ila tana kuskure idan har tana tsammanin cewa Hizbullah yana cikin matsala, kuma abinda na ke fadawa Isra’ila shi ne cewa; Wadanda su ka kashe Shahid Laqis ba za su kasance a cikin aminci ba a ko’ina su ke a duniya, domin lokacin daukar fansa yana tafe.” Da ya koma magana akan hare-haren bayan nan da ‘yan alkaeda su ka kai wa sojojin kasar ya yi kira da bada cikakken goyon baya ga sjojin domin su ke garkuwar kasar.

 

http://hausa.irib.ir/labarai/item/22785-lebanon-hizabullah-ta-sha-alwashin-daukar-fansa-akan-wadanda-su-ka-kashe-kwamandanta

Write a comment

Comments: 0