Saudiyya Tana Cikin Fushi Saboda Cimma Manufarta A Siriya

13Hausa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kasar Saudiyya tana cikin tsananin fushi sakamakon rashin cimma manufarta ta kifar da gwamnatin Siriya duk kuwa da kokarin da ta yi ba dare da ba rana wajen cimma wannan manufar.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin tunawa da shekaru 25 da kafa asibitin Rasulul A’azam a kasar Labanon inda yayi ishara da shan kashin da kasashen da suke adawa da gwamnatin kasar Siriya suke fuskanta a kokarin da suke yi na kifar da gwamnatin kasar wanda ya ce hakan shi ne ya fusata kasar Saudiyya sakamakon gazawar da ta yi na cimma manufarta ta kifar da gwamnati ta hanyar amfani da dukiya da kuma ‘yan ta’addan da take shigo da su Siriya daga kasashe daban-daban na duniya

http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/22249-sayyid-nasrallah-saudiyya-tana-cikin-fushi-saboda-cimma-manufarta-a-siriya

Write a comment

Comments: 0