Ya kira yi kasashen Saudiyya da Turkiya da su sauya siyasarsu

15- Hausa

Shugaban Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa; suna da kwararan dalilai akan wandanda su ka kai hari a unguwar Dhahiya da ke kudancin birnin Beirut.

A jawabin da ya gabatar dazunnan, Sayyid Hassan Nasrallah ya ce; wadanda su ka kai harin masu akidar kafirta musulmi ne, kuma suna da alaka da ‘yan tawayen kasar Syria. Jagoran na kungiyar Hizbullah ya kuma  yi ishara da tsokacin da shugaban kasar Turkiya Abdullah Gul ya yi, akan hatsarin da ke tattare da masu akidar kafirta musulmi a kasar Syria, sannan ya kara da cewa; An sanar da Gul ne cewa abinda ya ke faruwa a cikin kasar Pakistan zai iya faruwa a cikin Turkiya. Da ya ke maida martani akan zargin da ‘yan hamayyar Syria su ka yi na cewa; gwamnatin Syria ta bai wa Hizbullah makamai masu guba, Sayyid Nasarallah ya ce; Akida ta addini da kungiyar Hizbullah ta ke riko da ita, ta haramta mata mallaka balle amfani da wadannan irin makaman.

Har ila yau, Sayyid Nasrallah, ya yi ishara da cin kasar da kasashen da ke goyon bayan ‘yan ta’adda a Syria su ka yi, na kasa kifar da gwamnati, abinda ya ingiza su ga yin tuhuma mara tsuhe da cewa; HIzbullah ta mamaye Syria. Jagoran na Hizbullah ya ce babu wanda zai gaskata cewa kungiyar ta Hizbullah tana da karfin da za ta iya  mamaye  kasa kamar Syria. Jagoran kungiyar ta Hizbullah ya yi kira ga kasashen Saudiyya da Turkiya da su sake siyasarsu ta ina- da- yaki, domin kuwa yanayin siyasar yanki da duniya baki daya ya sauya.   

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21888-sayyid-hassan-nasrallah-ya-kira-yi-kasashen-saudiyya-da-turkiya-da-su-sauya-siyasarsu

Write a comment

Comments: 0