Sayyid Hasan Nasrullahi Ya Bayyana Hatsarin Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kudancin Labanon

13- Hausa

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya bayyana harin da aka kai kudancin kasar Labanon da cewar harin ta'addanci ne mai hatsari.     

A jawabin da ya gabatar a bikin tunawa da gagarumar nasarar da kungiyar Hizbullahi ta samu a yakin kwanaki 33 da ta yi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin watan Yulin shekara ta 2006 a garin Aita-Sha'ab da ke kudancin kasar Labanon a yau Juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar ga dukkan alamu masu dauke da ra'ayin kafirta musulmi ne suka aiwatar da harin ta'addancin da aka kai kudancin birnin Beiruit a jiya Alhamis da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 22 tare da jikkata wasu 330 na daban.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21483-sayyid-hasan-nasrullahi-ya-bayyana-hatsarin-harin-ta-addancin-da-aka-kai-kudancin-labanon

Write a comment

Comments: 0