Sayyid Nasrullahi Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Haramtacciyar Kasar Isra'ila

14- Hausa

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon ya jaddada cewar haramtacciyar kasar Isra'ila barazana ce ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, don haka shafe ta daga kan doron kasa masalaha ce ga dukkanin kasashen yankin.

A jawabinsa ga dubban jama'a a yayin taron gangamin ranar Qudus ta duniya a kudancin birnin Beirut na kasar Labanon a jiya Juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi ya jaddada cewa; dole ne al'ummar musulmin duniya su fi ba da fifiko kan batun 'yantar da Palasdinu saboda haramtacciyar kasar Isra'ila ba kawai barazana ce ga Palasdinu ba, domin cutar kansa ce mai yaduwa da take da mummunar hatsari ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21331-sayyid-nasrullahi-ya-jaddada-wajabcin-kawo-karshen-haramtacciyar-kasar-isra-ila

Write a comment

Comments: 0