Ya Yi Watsi Da Matakin Kungiyar Tarayyar Turai A Kan Hizbullah

18- Hausa

Babban magatakardar Kungiyar HIzbullah Sayyid Hassan Nasarllah ya yi watsi da matakin tarayyar turai wanda ya shigar da kungiyar ta gwagwarmaya a karkashin sunayen 'yan ta'adda. A wani jawabi da jagoran na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ya yi a yayin bud-bakin shekara-shekara, Sayyid Hassan Nasarallah ya ci gaba da cewa; Abu guda mai muhimmanci  shi ne cewa kungiyar tana da cikakken goyon bayan al'ummarta.

Jawabin na Sayyid Hassanrallah shi ne na farko bayan da kungiyar tarayyar turai ta shigar da bangaren soja na kungiyar Hizbullah a karkashin sunayen kungiyoyin ta'adda. Ya kuma bayyana cewa babu wata moriya da turai za su ci daga wannan matakin da suka dauka. Dangane da cikin gida Lebanon kuwa, Sayyid Nasarallah ya kirayi masu adawa da Hizbullah da su kwana da sanin cewa ba za su iya amfani da wannan matakin ba domin cin moriyarsa a siyasance.

http://hausa.irib.ir/labarai/item/21233-sayyid-hassan-nasrullah-ya-yi-watsi-da-matakin-kungiyar-tarayyar-turai-a-kan-hizbullah

Write a comment

Comments: 0